16 Janairu 2022 - 13:38
​Ana Samun Gagarumin Ci Gaba A Shirin Sake Kyautata Dangantaka Tsakanin Iran Da Saudiyya

Wani dan majalisar dokokin Iran ya ce Iran da Saudiyya sun dukufa wajen farfado da alakar kasashen biyu da suka yanke shekaru biyar da suka gabata saboda batutuwa da dama, da kuma shirin sake bude ofisoshin jakadanci a tsakninsu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya Asabar, dan majalisar dokokin kasar Iran mai kula da harkokin tsaron kasa da manufofin harkokin wajen kasar Jalil Rahimi Jahanabadi ya ce; maido da alakar da ke tsakanin muhimman kasashen Iran da Saudiyya za ta taka rawa wajen sassauta lamurra da dama a yankin.

Ya ce; farfado da dangantakar dake tsakanin muhimman kasashe biyu na Iran da Saudiyya, da kuma sake bude ofisoshin jakadancinsu, zai taimaka wajen kara samar da fahimtar juna da kuma hadin kan al’ummar al’ummar musulmi.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera da aka watsa a ranar 6 ga watan Janairu, ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce, ya zuwa yanzu Tehran da Riyadh sun gudanar da zama sau hudu, an gabatar da shawarwari masu inganci da ma'ana.

Ya bayyana cewa Iran a shirye take domin maido da hulda da Riyadh a kowane lokaci, ya kara da cewa Iran na maraba da sake bude ofisoshin jakadanci da karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Tehran, da kuma na Iran a Riyadh.

342/